ABNA24 : Jaridar ‘The Nation’ ta kasar Kenya ta bayyana cewa a cikin watan decemban da ya gabata ne kasashen biyu suka sami sabani mai tsanani dangane da yadda yan gudun hijira na Somaliya suka zama matsalar tsaro ga kasar Kenya.
Gwamnatin Uhuru Kenyata ta na ganin sansanonin ‘yan gudan hijiran kasar Somalia na Dadaab da kuma Kakuma suna barazana ga harkokin tsaro a kasar.
Amma a dayan bangaren kuma dokokin kasa da kasa sun hana maida ‘yan gudun hijira kasashensu da karfi, musamman a lokacinda zaman lafiya bai tabbata a kasar ba.
A cikin shekaru 3 da suka gabata ne, hukumar yan gudun hijira ta MDD ta sami damar maida ‘yan kasar Somalia kimani 28,000 kacal daga fiye 600,000 gida, saboda rashin zaman lafiyan da kasar take fama da shi.
Wadannan sansanonin ‘yan gudun hijira na Somalia dai sun kai fiye da shekaru 30 da bude su.
342/